Daga Sani Ibrahim Maitaya.
A Najeriya ƙungiyar kwadago ta ƙasar reshen jihar Zamfara, ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar 1 ga watan Disamba, idan gwamnatin jihar ba ta soma biyan mafi karancin albashi na dubu 70 ba, a ƙarshen wannan wata.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan da kammala taron majalisar zartaswar ƙungiyar a Gusau.
Ƴan Bindiga Sun Halaka Askarawa 8 A Jihar Zamfara.
Fadar Shugaban Najeriya Ta Karrama Shugaban Makarantar Sakandare A Jihar Zamfara.
Wakilin mu ya rawaito a makon da ya gabata shugaban ma’aikatan jihar Barista Ahmad Liman, ya ba da sanarwar cewar gwamnatin jihar za ta biya mafi ƙarancin albashin, amma sai an kammala binciken ma’aikata da ake kan gudanarwa, tare da kafa kwamitin da zai yi nazari kan batun.