Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wata ƙungiyar limaman Juma’a mabiya ɗariƙar Qadiriyya a Najeriya sun Buƙaci kamfanin samar da Man Fetur na ƙasar NNPCL ya sassauta farashin Mai cikin gaggawa, don sama wa al’ummar ƙasar da ke shan wahala sauki, sanadin ƙarin kuɗin Mai.
Kungiyar ta ce kiran nasu ya zama wajibi domin nema wa al’umma sauƙi daga matsananci halin matsin tattalin arziki da suke ciki, wanda ya haifar da tashin farashin kayan masarufi.
A cikin wata takardar manema labarai wadda ta aikowa Martaba FM Online, nai ɗauke da sa hannun sakataren kungiyar Malam Umar Dahiru Soron Ɗinki, limaman sun nuna kaɗuwa da mamakin ƙarin kuɗin Man da yazo a gaɓar da ƴan ƙasar ke kokawa da tarin matsaloli.
“Amma amaimakon muji an rage farashin sai kawai aka wayi gari da ƙari wanda yin hakan zai ƙara ta’azzara yanayin da yan kasa ke ciki,” in ji sanarwar.
Zancen Man Fetur Ya Sauka Zai Yi Wahala, -Ɗangote.
SSANU Ta Sake Yin Kira Ga Gwamnatin Najeriya Kan Biyan Albashin Watanni 4 Da Aka Hana Su.
Gwamnatin Najeriya Ta Bai Wa Ƴan Kasuwa Wa’adin Tata Ɗaya Su Rage Farashi.
Limaman sun kuma ba wa gwamnati shawara kan ta ɗauki matakin gaggawa da zai rage hauhawar farashin Man Fetur da ake yawan samu a Najeriya, suna masu cewa ya kamata gwamnatin ta yi abubuwa guda 4 da suka yi imanin za su taimaka wajen kawo sauki.
1.Gaggauta gyara matatun mai na ƙasa domin samun damar tace Man da ake haƙowa wanda zai jawo sauƙin sa da wadatarsa a kasuwa, kuma zai ƙarawa Gwamnati kuɗin shiga da rage dogaro ga ƙasashen waje.
2.Tabbatar da hana cin hanci da rashawa a harkar Man Fetur
3.Daidaita farashin Man Fetur a dukkan gidajen Mai na Gwamnati da na ƴan kasuwa.
4.Ƙirkirar sabbun dabaru da za su rage dogaro da Man Fetur a masa’antunmu da ma ababan hawa.
Kiran na su na zuwa ne ya yin da ƴan Najeriya ke ƙara kokawa da tsadar Man Fetur da kuma shan dogayen layuka a gidan Man ƙasar, ƴan kwanaki kaɗan da NNPCL ya ƙara kuɗin Mai a ƙasar daga 617 zuwa 897.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.