Daga Suleman Ibrahim Moddibo.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce za a cigaba da luguden wuta a kan ƴanbindiga da ɓarayin daji da masu satar man fetur da sauran ɓata-garin da suke addabar Najeriya matuƙar ba su daina ta’addancin da suke yi ba.
BBC Hausa ta rawaito, Tinubu ya bayyana hakane a ranar Alhamis a cibiyar samun horo na sojoji ta Army Resource Center da ke Abuja a wajen taron tattaunawa a kan matsalolin tsaro a Najeriya da hanyoyin magance su wanda kamfanin dillanci labarai na Najeriya NAN ya shirya a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami.
Tinubu wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce, “shekara 15 ke nan muna fama da rashin tsaro a Najeriya, mugayen mutane suna yadda suke so, amma yanzu lokaci ya zo da dole su dakata haka.
“A shekara ɗaya da ta gabata, an kashe sama da kwamandojin Boko Haram 300, sannan an samu sauƙin garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, don haka wannan gargaɗi ne gare su, sun dai ga yadda aka yi da kwamandojinsu, don haka idan suka ƙi miƙa wuya, za su fuskanci abun da ya faru da jagororinsu”, in ji shi.
“Ƙofarmu a buɗe take ga duk wanda yake so ya miƙa wuya, idan ba haka ba kuma, sun san abin da zai biyo baya,” in ji shi.
Kwanakin Bello Turji Sun Kusa Ƙare Wa- Sojin Najeriya.
Najeriya Ta Fi Samun Tsaro A Mulkin Tinubu -Nuhu Ribadu.
Sojojin Nijar Sun Kashe Ƴan Bindiga 60
Wasu sassan Najeriya dai na mafa da matsalar yan bindigar daji da masu garkuwa da sa satar man fetur gami da tayar da kayar baya, to sai dai a baya-baya nan gwamnatin ƙasar na cewa ta na yin nasara a yaƙin da take yi da su.