Yan majalisar wakilai 15 cikin 18 da aka zaba a jam’iyyar NNPP a jihar Kano sun amince da tsige dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Dala, Ali Madaki, a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.
A cikin wata takarda da DAILY NIGERIAN ta gani a yau Litinin, ƴan majalisar da ba su amince da cire Madakin Gini dinba su ne Alhassan Rurum na Rano/Kibiya/Bunkure da Abdullahi Sani na Karaye/Rogo.
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.
Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.
Kano Pro-pa ta nemi Gwamnatin Kano ta tsayar da ginin wasu ajujuwan karatu.
A cikin wata wasika da aka aika zuwa ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, tare da hadin gwiwar shugaban jam’iyyar NNPP da sakataren jam’iyyar NNPP Ajuji Ahmed da Dipo Olayoku, shugabannin jam’iyyar sun gabatar da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado, Tijjani Jobe, a matsayin wanda zai maye gurbin Madakin Gini.
“Mun rubuta wannan wasika ne domin mika sunan babban dan jam’iyyar mu, HON TIJANI ABDULKADIR JOBE domin maye gurbin Hon Aliyu Sani Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar,” wani sashe na wasikar ya ce
Duk da cewa ba a bayar da dalilin tsige Madaki ba, jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa hakan ba ya rasa nasaba da cewa Madaki a kwanakin baya ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya, kuma ya yi mubaya’a ga wanda ya kafa jam’iyyar, Boniface Aniebonam.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kuɗin hutu na 2024: Ma’aikatan Soba sun yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa biyansu akan lokaci.
-
Kwastam za ta ɗauki sabbin ma’aikata 3,927 a Najeriya.
-
Gobara ta ƙone kasuwar Babura ta Yar-Dole da ke jihar Zamfara.
-
Matatar Dangote haɗin gwiwa da kamfanin mai na MRS za su sayar da fetur a kan N935 duk lita.
-
Sojojin Nijar sun kashe Mahara 29 a Tillaberi.