April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ƴan Sandan Jigawa sun kama ƴan fashi tare da kwato baburan hawa.

Rundunar Ƴan Sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da fashi da makami, tare da kwato babura guda biyu da aka sace.

Kakakin rundunar SP Shi’isu Adam ya bayyana cewa, an kama waɗanda ake zargi ne bayan samun bayanai daga masu kwarmato masu bayanai da kuma gudanar da bincike mai zurfi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi a Dutse babban birnin jihar, SP Adam ya ce lamarin na farko ya faru ne a ranar 5 ga watan Maris 2025, lokacin da wasu ‘yan fashi suka farmaki wani mai babur mai suna Idris Ya’u, suka kuma kwace masa babur ɗinsa kirar Bajaj mai launin ja da lamba TRN 704 QL Kano.

“Mun kama wanda ake zargi mai suna Haruna Alhaji Yusuf a ranar 12 ga watan Maris 2025, kuma ya amsa laifin sa,” in ji SP Adam.

A wani lamari makamancin haka kakakin Ƴan Sandan ya ce wani mai babur mai suna Yunusa Suleman, shima ya fuskanci irin wannan hari a ranar 13 ga watan Maris 2024, in da aka kwace masa babur ɗin sa.

Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargi, mai suna Magaji Mohammed tare da babur ɗin da aka sace.

Binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa, Magaji Mohammed ya ɗauki wani mai babur kuma ya buƙaci ya kai shi Unity Pentagon Roundabout da ke kusa da gidan gwamnati.

“Da suka isa yankin Dasina Quarters inda abokin laifin sa yake, ya bukaci mai babur ya tsaya. A nan ne wani mutum mai suna Suleiman Nasaru wanda yanzu haka ake nema ruwa jallo, ya fito ya buge mai babur a kai da guduma.

“Sakamakon haka, mai babur din ya faɗi ƙasa ya suma, sannan masu laifin suka tsere da babur ɗin. Daga baya an garzaya da wanda aka garzaya da shi zuwa asibiti domin samun kulawa.”

Rundunar ‘yan sandan ta yaba da haɗin gwiwar kungiyar ƴan banga, waɗanda suka taimaka wajen kama waɗanda ake zargi.

Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa, “Ana ci gaba da bincike kan waɗanda ake zargi, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a kotu domin fuskantar hukunci.”

SP Adam ya tabbatar da cewa rundunar tana ƙoƙarin tabbatar da tsaro a jihar, tare da yin kira ga jama’a da su ba da bayanan sirri da za su taimaka wajen cafke sauran masu laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *