Daga Sani Ibrahim Maitaya
Rundunar Ƴansandan jihar Zamfara ta kama wani dan kasar Aljeriya mai shekaru 58 da ake zargi da safarar makamai, in da aka kwato bindigu kirar AK47 guda 16, da wasu ƙanana biyu a hannun sa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Dalijan ya bayyana haka, a lokacin da ya ke gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai, a hedikwatar ƴansanda da ke Gusau a ranar Talata.
Mista Dalijan ya ce Ƴansandan sun kuma kama wasu da ake zargi da sayar da babura da harsasai ga ‘yan bindiga, dauke da tsabar kuɗi naira miliyan biyu da rabi.
Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaddamar Sabuwar Tashar Mota Ta Zamani.
Ƙungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jihar Zamfara.
A cewar sa, sauran waɗanda aka kama sun haɗa da wasu da ake zargi da haƙar ma’adinai ta haramtacciyar hanya.
Ya ce ‘yan sandan sun yi aiki ne da sahihan bayanai da ke nuni da cewa ƴan bindigar sun shirya siyen babura da dama ne a hannun wadanda aka kama.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Akwai Bindigogin AK47 Guda Dubu 60 A Sansanonin Ƴan Bindiga Ɗari 120 Cikin Jihohin Arewa Masu Yamma,-Rahoto.
-
Wani Babban Kwamandan Sojin Isra’ila Ya Baƙunci Lahira A Gaza.
-
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.
-
Mutum Sama Da 20 Sun Mutu A Wani Harin Da Sojoji Su Ka Kai Kasuwa A Sudan.
-
Hezbollah Ta Fatattaki Sojojin Isra’ila A Ƙoƙarinsu Na Kutsawa Lebanon.