Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa Na Jam`Iyyar APGA Ya Bukaci Sarkin Muslmi, Shugaban Kiristoci Su Umarci Yan Najeriya Su Yi Azumi.

Page Visited: 1277
0 0
Read Time:1 Minute, 15 Second

Daga Ummahani Ahmad Usman

An yi kira ga sarkin Musulmi na Najeriya da shugaban Kiristoci na kasa da su umarci `yan Najeriya su yi Zzumi na kwanaki uku tare da addu`o`in neman zaman lafiya ga `kasa baki `daya.

`Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam`iyyar APGA Abdullahi Muhammad koli ne ya yi kiran cikin wani Shirin kai tsaye da aka yi da shi a shafin Martaba FM na facebook wanda Suleman Ibrahim Modibbo, ya jagoranta.

“kira na farko mu zauna lafiya, kuma wallahi muna bukatar shugabanni su sa mu yi azumi kan matsalolin da kasar nan take ciki, koda na kwana uku ne da niyar Allah ya kawo mana karshe hakin da muka samu kanmu, shugabanni musamman su Sultan na Sokoto da su shugabannin kiristoci ya kamata mu yi addu`a bai daya wa kasar nan,” in ji Koli.

Abdullahi Koli Ya Zama Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa A Jam’iyyar APGA.

Tsaro: Yakamata Iyaye Su Zuba Ido Kan Ƴaƴan Su -Koli.

Dan Me Yasa Ba Za A Yi Ƙungiyar Taimakawa Buhari Ba? -Koli.

Ya kuma yi kira ga `yan Najeriya su bawa jam`iyyar su goyon baya `dari bisa `dari domin acewarsa suna da manufofi masu kyau wa`danda za su kawo sauyi mai `dorewa a Najeriya ba tare da kawo banbanci ba.

Kiran na Koli, na zuwa ne yayin da harkokin tsaro ke cigaba da tabarbarewa a Najeriya musamman Arewa maso Yammacin kasar da ke fama da matsalar rigimar Hausawa da Fulani da kuma `yan bindigar daji.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

2023: Ƴan Takarar Shugabancin Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.

Ƴan Takaran zaben shugaban kasar Najeriya da za’ayi a shekara mai zuwa, yau sun rattaba hannu akan yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe da kuma tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Yayin wani biki da akayi a birnin Abuja da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta, ‘yan takarar zaben da suka […]

Read More
Siyasa

Ƴan Sanda Sun Gargaɗi Masu Ɗauƙar Makamai Da Kayan Maye A Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar yan sandan jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya, ta ja hankalin yan siyasa bisa yaƙin neman zaɓe mai tsafta. Jan hankalin rundunar ya zo ne a dai dai lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta buɗe damar yaƙin neman zaɓe a hukumance. Kwamishinan ƴan sandan […]

Read More
Siyasa

Kishin Ƙasa Shi Ne Tubalin Jagorancin Al’umma, Raunin Jagoranci Shi Ke Haifar Da Rashin Adalci,-Obasanjo.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake gudanar da mulki. Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito tsohon shugaban na wannan maganar a wurin taron bikin cikar makarantar Kings college ta Legas – daya daga cikin tsoffin makarantu a kasar – shekara 113 da kafuwa. Mista […]

Read More