April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ɗiyata “ta yi aiki wa Buhari shekaru huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ko kwabo ba-Buba Galadima

Buba Galadima wani jigo a jam’iyyar NNPP kuma ƙusa a gidan Kwankwasiyya, ya bayyana yadda diyar sa ta samu aiki a Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Ƙasa (NUPRC) ta hannun Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana hakan ne yayin wani shiri da aka gabatar a gidan talabijin na AIT.

Galadima ya ce duk da yawan suka da yake yi wa gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu akwai abokanta tsakanin sa da Shugaba Tinubu.

Ya ce: “Mu abokai ne, kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambaya. Bari in faɗi gaskiya a talabijin na ƙasa. Diyata ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban Ƙasa, kuma ya ɗaga wayar yana tsammanin ni ne. Suka ce su ‘ya’yana ne, kuma suna kiran sa ne saboda ƙasar ta yi tsanani.

“Suka gaya masa cewa mahaifin mu ba zai iya yi mana wannan ba, kuma ya gaya mana cewa kai abokin sa ne’.

“Ɗiyar ƙarama ta ce ta gama hidimar ƙasa (NYSC), amma ba ta samu aiki a
Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Ƙasa (NUPRC) ba, wacce Gbenga Komolafe ke jagoranta. Shi (Tinubu) kawai ya ce, ‘ku kira Komolafe’, ku ba wa diyata aiki. Shi ya sa take son zuwa Makka domin ta gode wa Allah da kuma Shugaban Ƙasa.”

Yayin da yake ci gaba da bayani, Galadima ya ce ya yi aiki wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na tsawon shekaru 13, yayin da diyar sa ta yi aiki na shekaru 4 ba tare da an biya ta albashi ba.

“Diyata ta yi aiki na tsawon shekaru huɗu, kuma ya yi umarni kada a biya ta albashi”.

“Su kawo shaida da aka biya ta. Ta yi aiki wa Buhari shekaru huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ko kwabo ba,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *