Kara zamin Ministan Gidaje da Ci gaban BiraneYusuf Abdullahi Ata, ya soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 Rabiu Musa Kwankwaso, kan furucin sa dangane da ayyana dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar Rivers.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin yada labarai Seyi Olorunsola ya fitar, ministan ya shawarci Kwankwaso da ya rike ra’ayin sa a zuciyar sa, yana mai cewa matakin da Shugaban kasa ya dauka na da muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali, da dimokuradiyya da kuma tsaron kasa.
Ministan ya kara da cewa jama’a su fahimci cewa, wannan mataki ya zama dole domin tabbatar da doka da oda a jihar Rivers, wacce ta dade cikin rudani na siyasa da rikice-rikice.
Haka kuma ministan ya yabawa Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai bisa amincewa da dokar ta-bacin cikin gaggawa.
“Majalisa ta yanzu tana dauke da kwararru da ke da nazarin rahotannin tsaro cikin lokaci da zurfin tunane domin hana rikici yin kamari; Wannan ya bambanta da Kwankwaso, wanda bai yi wani tasiri ba a tsawon shekarun sa hudu a Majalisar Dattawa,” in ji Ministan.
Ya kuma ce abin takaici ne ganin cewa Kwankwaso mutum ne da ba ya da fahimta mai zurfi game da doka da mulki, ya shawarce shi da ya mayar da hankalin sa kan magance rikicin da ke ci gaba da ta’azzara a Masarautar Kano, wanda shi da kansa ya haddasa ta hannun almajirin sa na siyasa Gwamna Abba Kabir Yusuf.
“A fili yake cewa Shugaba Tinubu ya yi aiki ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasa na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya ba shi damar aiwatar da matakan dokar ta-baci tare da tabbatar da kulawar doka, ta hannun majalisa a cikin wa’adin da aka kayyade. Kowace jiha da ke fama da rashin zaman lafiya mai tsawo ya kamata ta dauki darasi ta magance matsalolin ta na cikin gida,” in ji Ata.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Jam’iyyar SDP ta ce ba za ta shiga wata haɗaka ba a zaɓen 2027.
-
NNPP ta nesanta ta da Kwankwasiyya da su ƙungiyoyi ta na mai gargadin su dena bayyana kansu a matsayin cikakkun ƴaƴan jam’iyyar.
-
PDP ta sake dage taron Kwamitin Zartaswar ta na Kasa (NEC) zuwa ranar 15 ga watan Mayu.
-
Mijin Sanata Matasha ya buƙaci Akpabio da ya girmama matar sa.
-
Tinubu ya ya tabbatar da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya na farfaɗo wa.