Majalisar Wakilai a ranar Alhamis ta amince da karatu na biyu na dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati da Ofishin Shugaban Kasa a matsayin Shugaban Ƙasa, tare da samar da tsari kan yadda za a gudanar da zaɓen waɗannan mukamai da sauran batutuwan da suka shafi hakan.
Tun a shekarar 2024, ‘yan majalisa 60 daga jam’iyyun siyasa daban-daban, sun yi ƙoƙarin dawo da tsarin mulkin majalisa (parliamentary system), sun mai da hankali kan tsadar tsarin mulkin shugaban ƙasa (presidential system).
Daga nan suka ziyarci manyan shugabanni ciki har da mai alfarna sarkin musulmi Sa’ad Abubakar na III, da tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Ango Abdullahi, da wasu da dama domin neman goyon baya ga wannan yunkuri.
Sun kuma yi nuni da cewa Najeriya ta fi yin nasara a zamanin Jamhuriyya ta Farko, lokacin da ake amfani da tsarin mulkin majalisa.
Kudirin dokar wanda Shugaban marassa rinjaye a Majalisar Wakilai Mista Kingsley Chinda, da wasu ‘yan majalisa 59 suka dauki nauyi, ya tsallake karatu na biyu a ranar Alhamis.
A halin yanzu, ‘yan majalisar na kuma neman goyon baya kan wani kudiri da ke neman sake duba yadda ake zaɓen gwamnoni, da mataimakan gwamnoni, da naɗa kwamishinonin jihohi tare da sauran batutuwan da suka shafi hakan.
Haka kuma, an sanya wani kudirin doka da ke neman rage tsawon lokacin da ake ɗauka wajen yanke hukunci a shari’o’in da suka shafi zaɓe, kafin a gudanar da shi, tare da kafa kotunan sauraron kararrakin zaɓe kafin zaɓuɓɓuka.
‘Yan majalisar suna kuma son a tsara yadda za a dakatar da ɗan majalisa daga ayyukan majalisa.
Wannan kudirin dokar ya biyo bayan dakatarwar wata shida da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da’a, bayan wata muhawara mai zafi tsakanin ta da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio a lokacin wani zaman majalisar.
An kuma amince da wani kudirin dokar da ke neman sauya tsarin rinjayen ƙuri’u a zaɓen Shugaban Ƙasa da Gwamnonin Jihohi, tare da batutuwan da suka shafi hakan, wanda ya tsallake shima karatu na biyu.
Wani kudirin dokar da ya tsallake karatu na biyu a ranar Alhamis, shi ne wanda ke neman bai wa majalisar dokoki ta tarayya da majalisun dokokin jihohi ikon kiran Shugaban Ƙasa da Gwamnoni, domin amsa tambayoyi kan batutuwan tsaro ko wasu batutuwan ƙasa.
Sauran kudirorin sun haɗa da wanda ke neman cire ikon yin rijista da sa ido kan jam’iyyun siyasa daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), tare da mayar da ikon ga Ofishin Rijistar Jam’iyyun Siyasa.
Majalisar ta kuma amince da wani kudirin doka da ke neman sanya lokaci na mika daftarin kasafin kudi, da sauran batutuwan da suka danganci hakan.
Mataimakin Kakakin Majalisar Benjamin Kalu, ya sanar da ‘yan majalisa da suka gabatar da kudirorin samar da sabbin jihohi cewa 31 ga Maris 2025 ne wa’adin mika bukatar su, kamar yadda doka ta tanada.
A halin yanzu an gabatar da bukatar kafa sabbin jihohi 30, amma babu daya da ta cika ƙa’idojin kundin tsarin mulki.
A bisa tsarin majalisa duk wasu kudirorin da suka shafi gyaran kundin tsarin mulki za a mika su ga Kwamitin Musamman na Duba Kundin Tsarin Mulki, wanda Mataimakin Kakakin Majalisa Benjamin Kalu ke jagoranta, domin ci gaba da aiki a kansu.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja
-
Fasinjojin wata mota huɗu sun riga mu gidan gaskiya wasu kuma sun jikkata a jihar Borno.