Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta soki ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers da Shugaba Bola Tinubu ya yi, tana mai bayyana matakin a matsayin “wanda ya saba wa kundin tsarin mulki” kuma barazana ga dimokuradiyyar Najeriya.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata wacce Shugaban kungiyar na kasa Afam Osigwe SAN ya sanya wa hannu, kungiyar ta jaddada cewa Shugaba Tinubu ba shi da iko a kundin tsarin mulki na cire gwamna da aka zaba, ko mataimakin gwamna, ko ‘yan majalisar dokoki na jiha a karkashin dokar ta-baci.
“Kundin tsarin mulki na 1999 bai bai wa Shugaban Kasa ikon cire gwamna ko mataimakin gwamna da aka zaba ba, ko ‘yan majalisar dokokin jiha karkashin hujjar dokar ta-baci,” in ji NBA.
“Maimakon haka, kundin tsarin mulki ya gindaya hanyoyi a fili kan yadda za a cire gwamna da mataimakin sa bisa tanadin Sashe na 188.
Sanarwar ta kara da cewa “Haka kuma, cire ‘yan majalisar jiha da rushe majalisar dokoki na bin dokokin kundin tsarin mulki da na zabe, wanda bai bayyana an bisu ba a wannan yanayi ba,”
Kungiyar ta jaddada cewa ko da yake Sashe na 305 na kundin tsarin mulki ya bai wa Shugaban Kasa ikon ayyana dokar ta-baci, amma kuma ya bayyana sharudda da matakan kariya da dole ne a bi don kauce wa take hakkin dimokuradiyya da na dan Adam.
Kungiyar ta bayyana cewa rikicin siyasa da ke faruwa a jihar Rivers bai kai matakin da zai wajabta saka dokar ta-baci ba, tana mai tambayar ko lamarin ya kai matsayin rushewar doka da oda gaba daya.
“Ayyana dokar ta-baci ba ya nufin cewa za a rushe ko dakatar da gwamnati ta jiha ba”.
“Kundin tsarin mulki bai baiwa Shugaban Kasa ikon cire ko sauya zababbun shugabanni ba, yin hakan kamar yin karfa-karfa ne wanda ke take tsarin mulkin tarayyar Najeriya,” sanarwar ta bayyana hakan.
NBA ta kuma nuna cewa ko da an ayyana dokar ta-baci, dole ne Majalisar Tarayya ta amince da ita a cikin wani takaitaccen lokaci.
Kungiyar ta bukaci Majalisar Tarayya da ta yi watsi da duk wani yunkuri da ba bisa doka ba na cire Gwamnan jihar Rivers da sauran shugabannin da aka zaba, tana mai gargadi cewa “dakatar da shugabanni a karkashin dokar ta-baci babban hatsari ne da zai iya zama hanyar hambarar da gwamnati a gaba.”
Kungiyar ta bukaci duk masu ruwa da tsaki, ciki har da bangaren shari’a, kungiyoyin farar hula, da kasashen duniya, da su sanya ido kan halin da ake ciki a jihar Rivers.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja