Ƙungiyar League of Northern Democrats (LND) wadda wasu ƴan siyasa daga arewacin Najeriya suka kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ta fara yunƙurin zama jam’iyyar siyasa domin fuskantar zaɓen shekarar 2027.
BBC ya rawaito ƙungiyar ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da gazawa wajen ciyar da Najeriya gaba, sannan ta buƙaci ƙungiyoyin kudancin ƙasar da su shigo su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ceton ƙasar.
An ruwaito cikin wata sanarwa, daga ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar, Dr Umar Arɗo, ya ce ƙungiyar ta LND za ta kawo sauyi tare da sake dawo da martabar ƙasar.
PDP ta sha alwashin kwace mulkin Najeriya a hannun APC.
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.
Ya ce rashin ingancin gwamnati ne ya jefa ƙasar cikin ƙangin talauci da rashin tsaro da rashin tabbas.
Sai dai tuni jam’iyyar APC ta mayar da martani, inbda daraktan watsa labaranta, Alhaji Bala Ibrahim ya ce su dai ko gezau, domin a cewarsa, rikiɗewar ƙungiyar zuwa jam’iyyar siyasa ba barazana ba ce ga jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
PDP ta sha alwashin kwace mulkin Najeriya a hannun APC.
-
Sallamar da Gwamna Abba ya yi wa Sakataren Gwamnati da Kwamishinoninsa 5.
-
Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.
-
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.
-
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.