Daga Sani Ibrahim Maitaya
Wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe jami’an ba da kariya ga al’ummar jahar Zamfara da aka fi sani da ASKARAWA su takwas, a wani harin kwantan ɓauna da suka kai a karamar hukumar mulkin Tsafe ranar Litinin.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidabwa mjiyar mu cewa, ‘yan bindigar sun yi wa Askarawan kwanton ɓauna ne, a shingen binciken su mai tazarar kilomita kaɗan daga garin Tsafe hedikwatar karamar hukumar, in da yace lamarin ya faru ne da misalin karfe goma na safiyar Litinin.
Ya kuma ƙara da cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu, wajen kwarmata wa ‘yan bindiga bayanai dangane da lamarin.
“Halin yanzu da na ke magana da kai, an kama wasu mutane biyu da ake zargin su na da hannu wajen haɗa baki da ‘yan bindigar, kuma an riga an kashe daya daga cikin su nan take bayan da jami’an tsaron al’ummar su ka kama su,” in ji shi.
Ya ce an kai gawarwakin 8 na jami’an tsaron al’ummar da ‘yan bindigar suka kashe a dakin ajeyi gawarwaki a babban asibitin garin Tsafe.
“Ya zuwa yanzu, gawarwakin jami’an tsaron al’ummar mu guda 8 da waɗanda ‘yan ta’addan suka kashe, an kai su a babbar asibitin Tsafe domin gudanar da jana’izar su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada”.
Shugaban hukumar Askarawa na jahar Zamfara janar LB Muhammad mai murabus ya ce kowace rana ana tare mutane akan hanyar Funtua zuwa Gusau kafin su fara aiki a shekarun baya, shi yasa ya tura yaran shi domin kula da hanyar wanda ya ce an samu sauki, haifar faruwar wannan lamarin.
“Abin da ya faru, daman Tsafe, ana yin garkuwa kowacce rana sau uku sau huɗu ana ɗauka, sai nace bari na zuba Askarawan a wurin, kaga sai mu hana su shigo wa su ƴan bindigar, sun fi wata da rabi a wurin ba a taɓa garkuwa ba, tun da na sa su a wurin.
“Da suka fahimci ana kawo su da safe ne da maraice su ke tafiya, sai suka zo su ka kwanta hurin, su ka yi musu kwantan ɓauna, yarana suna sauka daga mota shine su ka buɗe musu huta, ka ji abin da ya faru, mutum 8 aka kashe,” in ji LB Muhammad.
Kwanakin Bello Turji Sun Kusa Ƙare Wa- Sojin Najeriya.
Ƴan Bindiga: Ƙofarmu A Buɗe Take Ga Duk Wanda Yake So Ya Miƙa Wuya- Tinubu.
Fadar Shugaban Najeriya Ta Karrama Shugaban Makarantar Sakandare A Jihar Zamfara.
Kwamishinan yan sandan jahar Zamfara CP Muhammad Dalijan ya tabbatar da afkuwar lamarin a wata zantawa da muryar Amurka, in da ya buƙaci matafiya da su kantar da hankalin su domin an kara yawan jami’an tsaro a yankin.
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahar Zamfara, da su gaggauta tura karin jami’an tsaro yankin domin dakile ‘yan fashi da ke addabar babbar hanyar tarayya ta Gusau zuwa Funtua da ake yi kusan kullum.
Babbar hanyar ta tarayyar ta Gusau zuwa Funtua tana fuskantar munanan hare-hare, daga ‘yan bindiga kusan kullum a cikin ‘yan watannin nan.
Gwamnatin jihar Zamfara dai ta samar da Askarawan ne da nufin kakkaɓe ayyukan ƴan bindigar da suka jima suna addabar jihar da makwabtan ta.