April 6, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ƴan jam’iyyar APC sama da dubu 7 sun fice daga jam’iyyar zuwa PDP a jihar Bauchi.

Mataimakin Shugaban jam’iyyar adawa ta APC a karamar hukumar mulkin Dass ta Jihar Bauchi Yunusa Umar, ya jagoranci sama da mambobi dubu bakwai da dari biyar na jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheka tare da shi har da Shugaban Matasa na APC a karamar hukumar Yusuf Inuwa Bora, da Sakataren Jin Daɗi da walwala Isah Zakaria.

Leadership ta rawait, an karɓi waɗanda suka koma PDP a hukumance ranar Lahadi ta hannun Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar mulkin Dass Hon. Yusuf Sabo, da kuma Shugaban ƙaramar hukumar Hon. Muhammad Abubakar Jibo.

Yunusa Umar ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa suka bar APC shi ne kyakkyawan aikin da Gwamna Bala Muhammad ke yi tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *