Daga Abdul’aziz Abdullahi
Rundunar Ƴansandan Najeriya reshen jihar Ogun ta kama wasu mutane da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ta Aiye Confraternity ne da ake nema ruwa a jallo a yankin Ijebu-Ode da ke jihar.
PUNCH ta rawaito, a ranar Litinin ɗin da ta gabata cewa, jami’an rundunar na musamman sun cafke waɗanda ake zargin ne a ranar Alhamis yayin wani samame da suka kai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola, ya bayyana cewa, an kama waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne tare da wasu ’yan daba, da su ka yi ƙaurin suna wajen safarar miyagun kwayoyi, fashi da kuma satar gidaje.
Waɗanda ake zargin sun hada da Balogun Ibrahim, Towolawi Omotayo, Oshodi Oluwaseun, Nkechi John, Mustapha Aliu, Opeyemi Rasheed, da Mustapha Sikiru.
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
Odutola ya ce, “Rundunar SWAT ta samu bayanan sirri cewa ƴan ƙungiyar Aiye Confraternity, da aka fi sani da Black Ax Cult, waɗanda su ka daɗe suna sa ido a kansu, an gansu a kan hanyar Ogbo, Ijebu-Ode.
“A bisa wannan bayanin, an tura tawagar SWAT domin daukar mataki, wanda ya kai ga kama mutane bakwai da ake zargi.”
Yansandan sun ƙara da cewa, ana kan binciken ƴan ƙungiyar da aka kama domin ganowa tare da damke sauran waɗanda ake zargi a yankin.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.
-
Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba.