Rundunar ƳanSandan Jihar Edo a ranar Lahadi, ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Kelvin Izekor bisa zargin kashe matar sa Success Izekor mai shekaru 38, a Birnin Benin ranar Asabar.
A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga ƴan sanda tare da mazauna yankin da abin ya faru suna ɗaukar gawar matar, wadda ke da raunukan sara a kanta, daga dakinta zuwa cikin motar ƴan sanda.
An ce ma’auratan sabbin aure ne, kuma mazauna yankin sun kasa fahimtar abin da ya faru tsakanin su da ya kai ga kisan Success.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo Moses Yamu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya ce wasu fusatattu sun kusa kashe mijin kafin ƴan sanda suka isa wurin, suka kwantar da hankulan jama’a, sannan suka kama shi.
Yamu ya ce Kwamishinan ƴan Sanda na Jihar Edo Betty Otimenyin, ta nuna damuwa kan yawaitar samun tashin hankali tsakanin ma’aurata, sannan ta tabbatar wa da jama’a cewa za’a gudanar da bincike mai inganci kan mutuwar matar, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi bisa doka.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Shekara 1 har yanzu ba a fara cikakken aiki da yarjejeniyar fahimtar juna don kafa Cibiyar dashen Ƙoda a Abisitin koyawa na jami’ar Jos ba.
-
Gwamnatin jihar Nasarawa ta rufe fiye da asibitoci 20 da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba.
-
“Yara 3 daga cikin 10 suna cikin mummunar matsalar yunwa a Bauchi”-UNICEF.
-
Dan Tiktok ya kashe kansa a ƙoƙarin yin Challenge da ke yawo ka kafafen sada zumunta.
-
Dokin rundunar Sojin Najeriya mai muƙamin Sajan ya mutu a Kaduna.