Daga Sani Ibrahim Maitaya
Jami’an rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun ceto mutane goma sha biyu da aka sace, a wasu manyan ayukkan da suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.
Wadannan ayukka sun haifar da kama wasu mutane ukku da ake zargi ‘yan ta’adda ne, tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan goma, bindigogi, da harsasai, da sauran abubuwa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa a jihar Imo jami’an ‘yan sanda sun ci gaba da matsa lamba kan miyagun mutane da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a.
A cewar sa “A ranar 17 ga watan Afrilu 2025 da misalin ƙarfe 1:02 na dare, jami’an ‘yan sanda tare da haɗin guiwar masu gadin unguwa, sun samu bayanan sirri kuma suka kai samame a wata maboyar da ake zargin na ‘yan IPOB/ESN ne da ke titin Cameron Ubahu, a ƙaramar hukumar Okigwe.
“Da suka ga jami’an, waɗanda ake zargin ‘yan ta’adda ne suka bude wuta, inda aka yi musayar wuta kuma hakan ya kai ga cafke mutane ukku da aka bayyana da suna Onyekaba Ikenna Innocent dan shekara 21; Ugwu Ikenna shekara 31, da Ofor Kasarachi mai shekaru 37.”
‘Yan sandan sun ce abubuwan da aka samu a wurin sun haɗa da bindiga AK-47 guda ɗaya, da bindigogin pump-action guda biyu, da harsasai guda 18, da wayoyin hannu, da kwamfutocin hannu, da kuɗi ₦10.3 miliyan da ake zargin kudin fansa ne da aka yi garkuwa da mutane.
A wani cigaban kuma da ya faru a jihar Edo, bayan samun rahoton sace ɗalibbai goma (10) da ke kan hanyarsu zuwa Jami’ar Babcock Ilishan-Remo Ogun State, domin halartar taron shekara-shekara na GYC Africa a ranar 16 ga watan Afrilu 2025, jami’an ‘yan sanda na jihar nan da nan suka bi sahun masu garkuwa da mutane kuma suka fafata da su.
‘Yan sandan sun ce an kashe ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutane a fafatawar, sannan aka ceto dukkan ɗalibban goma cikin koshin lafiya ba tare da rauni ba.
Haka kuma a ranar 18 ga watan Afrilu 2025, da misalin ƙarfe 9:15 na dare, rundunar ta samu nasarar ceto wasu mutane biyu da aka sace a ranar 14 ga watan Afrilu 2025, a gidan su da ke unguwar Oluoke a cikin jihar.