2023: Ƴan Takarar Shugabancin Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.

Page Visited: 159
0 0
Read Time:59 Second

Ƴan Takaran zaben shugaban kasar Najeriya da za’ayi a shekara mai zuwa, yau sun rattaba hannu akan yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe da kuma tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Yayin wani biki da akayi a birnin Abuja da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta, ‘yan takarar zaben da suka hada da Atku Abubakar na PDP da Peter Obi na Jam’iyyar Labour da Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP sun rattaba hannu akan yarjejeniyar, yayin da Kashim Shettima dake marawa Bola Ahmed Tinubu baya ya sanya hannu a madadin sa.

Rashin bayyana Tinubu wajern bikin ya haifar da cece kuce daga wasu ‘yan Najeriya, musamman masu tsokaci a kafofin sada zumunta.

Shugaban Hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya bukaci sanya hannu akan yarjejeniyar ya zarce bikin da aka gudanar, wajen ganin tasirin sa, a tsakanin ‘yan siyasar da kuma magoya bayan su.

‘Yan takara 18 suke fafatawa domin maye gurbin shugaban kasar Muhammadu Buhari dake kawo karshen wa’adin mulkin sa a watan Mayu mai zuwa.

A ranar 25 ga watan Fabarairu za’a gudanar da zaben wanda ake saran mutane sama da miliyan 80 su kada kuri’a.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

Kwankwaso Ya Ƙaddamar Da Titin Da Wike Na PDP Ya Yi A Jihar Rivers.

Dan takarar shugaban kasa a tutar jamiyyar NNPP Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da aikin wani titi a karamar Emohua da gwamnan jihar Rivers na PDP Nyesom Wike yayiwa alummar jihar Rivers Yayin taron kaddamarwar dai Kwankwaso na tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa a NNPP Bishop Isaac Idahosa da Injiniya Buba Galadima […]

Read More
Siyasa

Zaɓen 2023: Za Mu Tabbatar An Gudanar Da Sahihin Zaɓe A Jihar Kano- Ganduje.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa al’ummar jihar Kano tabbacin cewa za a gudanar da sahihin zabe a zaben shekarar 2023 mai zuwa. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC da suka shirya gangami domin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na […]

Read More
Siyasa

Mace Ƴar Maɗigo Ta Zama Gwamna A Amurka.

Maura Healey ita ce mace ta farko da ke bayyana kanta da cewa ‘yar madigo ce an zaɓe ta a matsayin gwamna a jihar Massachusetts ta ƙasar Amurka. BBC Hausa ta rawaito Ms Healey mai shekara 51 ta kayar da abokin karawarta na jam’iyyar Republican Geoff Diehl, wanda ke samun goyon bayan tsohon shugaban kasar […]

Read More