April 2, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

A ƙalla mutum 7 hatsarin mota ya yi ajali a jihar Imo.

Mutum bakwai ake tunanen sun mutu bayan da motoci uku suka yi karo da juna a yankin Ulakwo, kan titin Owerri zuwa Aba, a daren Lahadi a jihar Imo bayan wani ruwan sama mai ƙarfi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo (PPRO) DSP Henry Okoye, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa jami’an ‘yan sanda sun je wurin don tabbatar da doka da oda.

“Eh, DPO da mutanen sa suna wurin don tabbatar da doka da oda, da kwashe gawarwakin, da kuma tabbatar da cewa zirga-zirgar ababen hawa na tafiya yadda ya kamata. Mun ɗauki matakan da suka dace kan lamarin,” in ji PPRO.

Rahoton LEADERSHIP ya bayyana cewa an samu ruwan sama mai ƙarfi misalin ƙarfe 5 na yamma, wanda ya haddasa cunkoso yayin da masu ababen hawa ke ƙoƙarin gujewa tsaikon hanya.

Wata majiya ta danganta hatsarin da rashin iya gani sosai da gaggawar direbobi yayin ruwan saman.

Ya ce, “Ko da yake titin yana da faɗi, ruwan sama ya sa hanya ta matse wanda ya haddasa haɗuwar motoci ukun da juna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar waɗanda suka rasa rayukkan su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *