Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
A Gaggauce Gwamnatin Kano Ta Bayyana Kama Abduljabbarr. - Martaba FM
October 20, 2021

A Gaggauce Gwamnatin Kano Ta Bayyana Kama Abduljabbarr.

Page Visited: 140
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:44 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kama Abduljabbar Kabara babban taimakawa gwamnan kan kafofin sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ne ya bayyana kama Abduljabbar din a shafin sa na facebook, inda yace “an kama Abduljabbar yanzu”.

Sai dai bai bayyana wace hukumance ta kama malamin ba, sai dai kawai yace za’a “gurfanar da shi gaban kotun addinin musulunci”.

A ranar Asabar data gabata ne gwamnatin jihar Kano ta shirya masa mukabala tsakanin sa da malamai a jihar wanda bayan gama mukabalar alkalin daya jagoranci mukabalar yace Abduljabbar bai amsa tambayoyin da malamai suka yi masa.

To amma a ranar Lahadin data gabata Abduljabbar ya fitar da sautin muryoyinsa guda yana cewa ya tuba ya janye kalamansa.

Gwamnatin iihar dai tace bata karbi tubansa ba.

Malamai a Kano dai na zargin Abduljabbar dayin batanci ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, wanda shi kuma yasha musanta hakan.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us