January 22, 2025

A Jihar Kano Kotun Musulunci Ta Yi Umarnin Coci Ta Rantsar Da Wani Kirista Da Littafin Bible.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wata babbar kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu karkashin Mai Shari Ibrahim Sarki Yola, ta ummarci wata Coci da ta rantsar da wani kirista mai suna Yakubu Tumoti, da littafin Baibul domin kaucewa zargin da wani matashi ya yi masa cewa sun bashi ajiyar mashin mai kafa 2 lifan an sace.

Arewa Radio ta rawaito cewa, tun da farko matashin mai suna Mahmud Yusuf Kofar Nasarawa, ya shigar da kara kotun yana neman ta kwato masa mashin dinsa da ya je Magaji Rumfa domin yin Booking na filin Bal da za suyi.

Anan suka tambayi Tumoti inda za su ajiye mashin din nasu kuma anan take ya nuna musu, sai dai bayan ajiyewar sun dawo dauka, sai su kaga babu mashin awajen ko da suka tambaye shi sai ya ce yaga wasu wai sun tura sun yi gaba dashi.

Ko da mai shari`a Ibrahim Sarki Yola, ya tambayi wanda ake zargin Tumoti sai yace shi sam ba su bashi wani ajiyar mashin ba hasalima shi bai taba ganin su ba tunda shi aikin sa awajan ya bude kofa a shigo ko a fita.

Tuni mai shari`a ya tambayi Tumoti cewa a matsayin sa na Kirista koya yadda ayi masa shari’a a kotu ta Musulunci ko a kai su majistire, nan take Yakubu Tumoti, ya ya roki da ayi masa shari’ar a kotun musuluncin.

Wanda hakan ya sa Sarki Yola, ya umarci Insifeto Sulaiman da daya daga cikin ma aikatan kotu da Rijistara da suje da Tumoti Cocin da ya ke gabatar da ibadar sa babban malamin sa ya rantsar da shi kan cewa bashi ne ya dauki babur din ba, kuma bai san wanda ya dauka ba, kana ba a hada kai dashi an dauka ba, hasali ma bai san suba.

Daga karshe mai shari Ibrahim Sarki Yola, ya dage cigaba da shari’ar zuwa ranar 4 gawatan 12 na wannan shekara da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *