April 1, 2025

A jiya Alhamis ne tsohon shugaban Najeriya Buhari ya koma gidansa na Kaduna da zama.

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya koma gidan sa da ke Kaduna bayan ya kwashe kusan shekaru biyu a mahaifar sa Daura Jihar Katsina.

Buhari ya koma zuwa garin Daura tun bayan barin mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Ɗaya daga cikin tsoffin hadiman sa a harkar yaɗa labarai Bashir Ahmad, shine ya bayyana hakan a shafin sada zumunta a ranar Alhamis, ya na mai cewa bayan kammala wa’adin mulkin sa na shekaru takwas, Buhari ya zabi rayuwa mai nutsuwa a garin su, inbda ya nisanci tattaunawar siyasa tare da mayar da hankali kan harkokin kansa.

Ya ce tsohon Shugaban ƙasar ya samu rakkiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da manyan mutane ciki har da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Zulum, da takwaran sa na Jihar Kaduna Uba Sani; da mataimakan gwamnan Jihar Katsina na yanzu da na baya, da tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, da tsoffin ministoci, da wasu daga cikin hadiman sa na kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *