Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa
Kungiyar Direbobin Tankokin man fetur, PTD, reshen kungiyar ma’aikatan matatar man fetur da iskar gas ta Najeriya NUPENG, sun karyata rahoton cewa mambobinta na shirin gudanar da zanga-zanga.
Shugaban PTD na kasa, Augustine Egbon, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mambobin kungiyar ba sa shirin yin kowace irin zanga-zanga.
Ya ja kunnen jama’a game da yadda wasu masu son zuciya da miyagu ke yi ruɗar su.
“Hakan ya haifar da firgici marar tushe da kuma hadari a cikin jerin hanyoyin rarraba albarkatun man fetur a kasar nan ta hanyar yada labaran karya da karya.
Mambobinmu ba sa shirin yin wata zanga-zanga kuma mun kuduri aniyar ci gaba da yi wa kasa hidima.
“Muna goyon bayan kokarin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi na dora tattalin arzikinmu kan turba mai kyau domin amfanin mu baki daya,”in ji shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.
-
Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata.