Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Ma’aikatar lafiya ta Gaza da ke karkashin ikon Hamas ta ce an kashe mutum 109 tun bayan karewar wa’adin tsagaita wuta na wucin gadi a safiyar Juma’a.

Ta kara da cewa an kuma jikkata daruruwan mutane.

Zuwa yanzu dai an kashe mutane sama da 14,800 a cikinsu har da yara kimanin 6,000, tun bayan hare-haren da Isra’ila ta fara kai wa Gaza don ruguza Hamas, wadda ta kaddamar da mummunan harin 7 ga watan Oktoba a kan Isra’ila.

An tsagaita wuta a Gaza ne domin shigar da kayan agaji da kuma kwashe marasa lafiya, a inda rikicin yafi kamari.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *