Wasu rahotanni daga jihar Jigawa na nuni da cewa, an samu ƙarancin mutane da za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomi da ke gudana a yau Asabar a jihar Jigawa.
Daily Trust ta lura cewa yayin da jami’an tsaro da na zaɓe su ka kasance a wasu rumfunan zaɓe, an bar su da jiran kayan zaɓen domin har zuwa wasu awanni al’umma ba su fito kada kuri’a ba.
A cewar Trust, haka abin yake a mazabar Jigawar Tsada, inda ma’aikatan zabe ke zaune tsuru-tsuru su na tsimayen masu zaɓe.