Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa
Kotun daukaka kara da ke zaman ta a Kaduna a ranar Alhamis, ta yi watsi da karar da ke neman cire Sarkin Zazzau na 19 Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
Wannan takaddama ta fara ne lokacin da tsohon mai nada sarki a masarautar Zazzau Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu, ya kalubalanci nadin Sarkin Zazzau da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi, a watan Oktoba na shekarar 2020.
Aminu wanda ya kasance Wazirin Zazzau kuma daya daga cikin wadanda suka taka rawa a tsarin zaben sabon sarki, ya yi zargin cewa ba a bi ka’ida ba wajen nadin Sarkin, don haka ya shigar da kara a babbar kotun jihar Kaduna, yana neman a soke nadin Bamalli da kuma tsige shi daga sarauta. Sai dai kotun farko ta yi watsi da karar.
A hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ta bayyana cewa, karar ta dade da kare wa bisa doka, ma’ana an shigar da ita bayan wa’adin da doka ta kayyade.
Kotun ta kuma yi watsi da hujjar cewa lamarin ya cancanci a dauke shi a matsayin na musamman, da za a tsawaita wa’adin shigar da kara.
Da yake mayar da martani kan hukuncin Wazirin Zazzau Khadi Muhammad Inuwa, wanda ya yi magana a madadin masarautar ya nuna jin dadin sa da hukuncin, yana mai cewa hakan nasara ce ga adalci kuma ya tabbatar da cewa kotu ita ce mafakar karshe ga talakawa.
A nasa bangaren lauyan wanda ya daukaka kara Muhammed Tajudeen Muhammed, ya ce zai nazarci hukuncin da kyau domin sanin matakin da za su dauka a gaba, tare da bai wa wanda yake tsayawa shawara.
Tajudeen ya jaddada cewa wanda yake karewa ya shigar da kara ne don tabbatar da cewa nadin Sarkin ya saba wa dokoki da al’adu na masarauta, amma kotu ba ta dauke shi a matsayin wani abu da ya cancanci tsawaita wa’adin shigar da kara ba.
A gefe guda Abdul Ibrahim (SAN) lauyan Sarkin Zazzau, ya karbi hukuncin da farin ciki, yana mai cewa kotun daukaka kara ta wuce matakin da kotun farko ta yi na kawai watsi da karar, inda ta yi fatali da ita gaba daya.
Ya bayyana hukuncin a matsayin cikakken tabbaci na sahihancin nadin Sarki Bamalli da kuma wata babbar nasara ga bin doka da oda.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja