January 22, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Aikin Da Aka Yi Na Gyaran Bakarantu Ba Gwamnatin Kano Ce Ta Yi Ba, Kuɗin AGILE Ne Na World Bank-Ƙiru.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kano a lokacin tsohuwar gwamnatin Ganduje, Muhammad Sunusi kiru, ya ce ba gwammatin Jihar Kano ce ke gyaran makarantu da ake gani ba a jihar, Shirin AGILE ke yi.

Da yake tsokaci a shafin sa na Facebook, Ƙiru ya yi zargin ana yi wa shirin AGILE na bankin duniya rinton aiki, “duk wani aiki da aka yi na gyaran makarantu ba gwamnatin Kano ce ta yi ba, kuɗin AGILE ne na World Bank da aka umarta ayi ta hannun SBMCs na waɗannan makarantun.”

Tsohon Kwamishinan ya yi martani ne kan irin ayyukan da jami’an gwamnati jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf, ke yaɗa wa a kafafen sada zumunta, suna bugar ƙirji da su.

Iyalan Sarkin Kano Ado Sun Ƙaryata Alaƙa Da Zainab Wadda Take Iƙrarin Ita Ɗiyar Sarkin ce.

Bidiyon Ɗan Bello: An Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma Da Wasu Manya A Kano.

Za A Ɗauki Ma’aikata Sama Da Dubu 40 Domin Aikin Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano.

Muhammad Ƙiru ya ce “Naga wasu daga Jami’an gwamnatin Kano suna ɗauko ayyukan da aka yi a makarantu suna danganta su da aikin da gwamnatin Kano ta yi bayan sun zo sun tarar da waɗannan ayyuka da kudaden ayyukan tun zamanin Gwamna Ganduje.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *