January 19, 2022

Al`ummar Jihar Kaduna Na Cigaba Da Bayyana Farin Cikin Su Da Ranar Mauludin Annabi

Page Visited: 134
0 0
Read Time:1 Minute, 9 Second

Daga Mu`Azu Abubakar Albarkawa

 

Ranar 12 ga watan rabi`ul auwal ta kowace shekara it ace ranar da al`ummar musulmi ke murnar ranar haihuwar Annabi Muhammad S A W, musulmi na aikewa yan uwa da abokai fatan alkairi da taya murna a fadin duniya.

Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya wasu daga cikin musulmin jihar masu yin Mauludin Annabi sun bayyana farin cikin su.

A Zariya da jihar ta kaduna garuruwa da anguwani suna gudanar tarukan mauludi, inda mai martaba sarkin zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya halarci taron maulidin.

Inda aka gudanar da addu’oi na zaman lafiya da yiwa kasa addu’ar samun cigaba.
Ibrahim Garba Umar Madalla, wani jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon ɗan takarar majalisar dokokin jihar Kaduna ya bayyana farin cikin sa game da zagayowar watan Mauludi.

Ibrahim Garba Umar Madalla, y ace, “Ina yiwa ‘yan uwa amintattun Musulman Najeriya dama na duniya baki daya barka da zuwa ranar Mauludin Annabi s.a.w tare da fatan Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da saukar da albarkar sa garemu Baki daya”.

“yayin da muke bikin tuna wa da wannan rana a Najeriya da duniya baki daya bari mu yi amfani da wannan damar domin sake rungumar kyawawan halayen Annabi Muhammad (saw) domin samun warka ga al’ummomin mu da sake gina tubalin tattalin arzikin cikin gida Nageriya da yayi Matukar lalacewa”.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *