January 31, 2023

Amaryar Ta Rasa Idonta Daya Ne Ana Tsaka Da Bikinta Sai Dai Duk Da Haka An Daura Mata Aure Da Angonta.

Page Visited: 170
0 0
Read Time:1 Minute, 0 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wata amarya mai suna Khadija Abdullahi, a unguwar Kwajalawa da ke birnin Kano ta rasa warin idonta daya a lokacin da ake tsakiyar bikinta ana gobe daurin aure.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin Kakinta Sifiritandan Yan Sanda Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya ce tini sun kama mutum biyu da ake zargi da aikata laifin.

Wanda ya ce kama mutum biyun ya biyo bayan korafi da amaryar Khadija ta shigar ga yan sanda ne tin a ranar 13 ga watan Junairu na shekarar 2023 da muke ciki “ ta shigar da karafi a ofishin yan sanda na Zango a kan cewa suna bikin aurenta sun kunna kidan DJ a kofar gida, wadansu yan Vigilanty su zo suka ce lallai fa sai an dena, sun hana wannan kidan DJ a unguwa, ta dalilin haka ne tana tasaye sai taji jifa a idonta,” in ji shi.

Kiyawa, ya kuma ce, an dauketa an kai ta asibiti inda likita ya tabbatar da cewa ta samu raunuka sama da kuma kasan idanun nata.

“Yanzu haka dai mun kama mutane biyu Yahaya da kuma salisu alhajin kwari da tini an gurfanar da su a gaban kotu, a cewarsa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *