Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Aƙalla mutum 49 ne suka mutu, sannan dubbai suka rabu da muhallansu bayan mamakon ruwan sama da ya jawo ambaliya a Arewacin Najeriya, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya ta sanar a ranar Litini.
BBC ta rawaito, a jihohin Arewa guda uku da suka fi fuskantar ambaliyar su ne Jigawa da Adamawa da Taraba, kamar yadda Kakakin NEMA Manzo Ezekiel ya shaida.
A shekarar 2022 ce Najeriya ta yi fama da ambaliya mafi muni a cikin shekakarar da suka gabata, in da mutum 600 suka mutu, sannan kusan mutum miliyan 1.4 suka rasa muhallansu, sannan aƙalla hekta 600 na gona ya lalace.
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi Ga Al’ummar Kiyawa.
Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.
“Yanzu ne muke shiga ƙololuwar damina, musamman a Arewacin ƙasar,” inji Ezekiel a tattaunawarsa da Reuters.