January 22, 2025

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi Ga Al’ummar Kiyawa.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Gwamnan jihar Jigawa a Arewacin Najeriya, Malam Umar Namadi, ya raba kayan tallafi ga al’ummar da bala’in ambaliyar Ruwa ya sha a ƙaramar hukumar Kiyawa ta jihar.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Facebook kwamishin Ayyuka na Musamman Auwal D. Sankara, ya ce, sun bayar da tallafin ne “domin rage musu raɗaɗin da suke ciki”.

“Muna matukar jimami da ambaliyar ruwa da ta addabi mazauna ƙaramar hukumar Kiyawa, a matsayina na kwamishinan Ayyuka na Musamman, ni da tawaga ta, mun ziyarci al’ummomin da abin ya shafa domin duba irin ɓarnar da ambaliyar ta yi da kuma bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa”, in ji shi.

Sankara ya kuma ce, tunaninsu da addu’o’insu na tare da al’ummar Kiyawa da duk wadandae ambaliyar ta shafa “mun himmatu wajen bayar da taimako da tallafi ga al’ummomin da wannan bala’i ya shafa a faɗin jihar Jigawa, mu cigaba da aiki tare, don taimaka musu da samar da hanyoyin hana afkuwar irin wannan bala’i a nan gaba”.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Jigawa, su ci gaba da haɗa kai domin tausayawa da ƙarfafa gwiwa da tallafa wa wanɗanda abin ya shafa.

Gwamnan ya miƙa tallafin ne ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *