April 18, 2025

Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Birnin Maiduguri.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wasu rahotanni da ke fitowa daga jihar Borno na cewa, al’umma mazaunin birnin Maiduguri sun shafe daren jiya ba tare da bacci ba, saboda mummunar bala’in Ambaliyar Ruwa da ta mamaye birnin.

Jama’a da dama ne suka taru a kofar fadar Shehun Borno, in da suke neman mafaka, ko da dai nan ɗin ma ruwa ya mamaye wani bangare.

Tini dai hukumar kashe Gobara da sauran hukumomi suka dukufa wajen shawo kan matsalar, in ake kai agajin gaggawa ga waɗanda bala’in ya shafa.

Daman Gwamnatin jihar ta yi ta wayar da kai mutane kan hasashen samun Ambaliyar Ruwan, in da Gwamna Umar Zulum ya bayar da umarni rufe makarantun Firamare da Sakandare a jihar domin kare yara daga barazanar Ambaliyar.

Hukumomi a Najeriya sun yi hasashen samun Ambaliyar Ruwa a wasu jihohin Najeriya 21 sakamakon ruwan da za a yi ta yi tsawon kwanaki ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *