Siyasa
Trending

Amnesty Ta Nemi A Saki Ɗan PDPin Da Ke Tsare A Sokoto Kan Wallafa Bidiyon Gwamna Da Matarsa.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin jihar Sokoto da hannu wajen kame wani matashi ɗan jam’iyyar PDP mai amfani da shafukan sada zumunta, Shafi’u Umar Tureta.

Daily Trust ta rawaito, a cikin wata sanarwa da ta fitar, Amnesty ta ce Ƴansandan suke dauke da muggan makamai suka kama matashin, bayan ya wallafa wani faifan bidiyo na “bikin zagayowar ranar haihuwar matar gwamnan.”

Kungiyar ta yi zargin cewa “a yanzu haka, ana shirin gurfanar da Shafi’u Tureta a gaban kotu, a ƙoƙarin neman kai shi zaman gidan yari na tsawon lokaci, tare da kirkir tuhume-tuhumen da ake yi masa na bogi.

“Dole gwamnatin jihar Sokoto ta gaggauta sakin Shafi’u Umar Tureta ba tare da wani sharaɗi ba, wannan yawaitar take hakkin dan Adam da gwamnatin jihar Sokoto ke yi ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma dole ne a kawo karshensa yanzu,” in ji Amnesty.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da ta ba da fifiko wajen magance talauci, yaran da ba sa zuwa makaranta da ke tashe-tashen hankula a titunan Sakkwato da kuma kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.

Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.

An Shekara Sama Da 5 Ba A Ɗauki Malami Ko Ɗaya Ba A Jihohin Najeriya 18 Ba-NUT.

A halin da ake ciki, jam’iyyar PDP a jihar ta kuma fitar da wata sanarwa in da ta buƙaci a gaggauta sakin dan majalisar.

Abubakar Baba, mai magana da yawun gwamna Ahmed Aliyu, bai amsa kiran da aka yi masa ba, ko kuma ya amsa sakon tes na neman ƙarin haske kan zargin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button