Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio, ya bayyana a ranar Asabar cewa ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya don hanzarta isar da taimakon soja, da ya kai kusan dala biliyan hudu ga Isra’ila.
Rubio ya ce gwamnatin Trump wacce ta karɓi mulki a ranar 20 ga wata Janairu, ta amince da kusan dala biliyan goma sha biyu na sayar da manyan makaman soja ga Isra’ila. Ya ƙara da cewa za su ci gaba da amfani da duk wata hanya da ake da ita don cika alkawarin tsawon lokaci na Amurka ga tsaron Isra’ila, ciki har da matakan da za su taimaka wajen magance barazanar tsaro.
Rubio ya bayyana cewa ya yi amfani da ikon gaggawa don hanzarta isar da wannan taimakon soja ga Isra’ila, wacce ke cikin wani yanayi mai sarkakiya na tsagaita wuta da mayaƙan Hamas a yakin da suke yi a Gaza.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta sanar a ranar Juma’a cewa Ma’aikatar Harkokin Waje ta amince da yiwuwar sayar da bama-bamai, kayayyakin fashewa, da sauran makamai da darajarsu ta kai kusan dala biliyan ukku ga Isra’ila.
Gwamnatin Trump ta sanar da Majalisa game da wannan yarjejeniyar sayar da makamai ta hanyar dokar gaggawa, wanda hakan ya kauce wa tsohuwar hanya da ke bai wa shugabannin kwamitocin harkokin waje na Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa damar duba cinikin kafin a sanar da Majalisa a hukumance.
Sanarwar ranar Juma’a ita ce karo na biyu cikin ‘yan makonnin da suka gabata, da gwamnatin Trump ta ayyana gaggauta amincewa da sayar da makamai ga Isra’ila cikin hanzari.
Haka kuma, gwamnatin Biden a baya ta yi amfani da ikon gaggawa don amincewa da sayar da makamai ga Isra’ila ba tare da duba Majalisa ba.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.
-
Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata.