An faɗaɗa hanyoyin jigilar jama’a a birnin Riyadh don haɗa Diplomatic Quarter, inda yawancin jakadun ƙasashen waje ke da ofisoshin su.
Sabbin hanyoyin bas za su fara aiki daga King Saud University zuwa Diplomatic Quarter, kowace rana daga ƙarfe 6:30 na safe zuwa 12:00 na dare.
Ana iya duba cikakken jadawalin tafiyar a cikin manhajar Darb na jigilar jama’a.
Wannan faɗaɗawar na zuwa ne a matsayin wani yunkuri na Hukumar Masarautar Raya Birnin Riyadh, wajen inganta hanyoyin sufuri a birnin.
Bayan ƙaddamar da Riyadh Metro a watan Disamba na 2024, wanda ke da layukka shidda masu ratsa fiye da kilomita 176, hukumar na ci gaba da ƙarfafa hanyoyin bas.
A halin yanzu, birnin ya na da fiye da tashoshi da wuraren tsayawar bas 2,860, waɗanda ke hada jimillar kilomita 1,905, tare da ƙarfin ɗaukar mutum 500,000 a kowace rana.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja