Yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 24.23 a cikin dari a watan Maris, in ji Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).

Rahoton da hukumar ta fitar ya bayyana cewa wannan ƙididdiga ta yi nuni da samun ƙarin kashi 1.05 cikin dari idan aka kwatanta da kashi 23.18 cikin dari da aka samu a watan Fabrairu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan shi ne karon farko da adadin hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru, tun bayan da NBS ta sake duba tsarin lissafin Consumer Price Index (CPI) a farkon shekarar nan.

“Idan aka dubi sauyin, adadin hauhawar farashi na watan Maris 2025 ya nuna ƙaruwa da kashi 1.05% idan aka kwatanta da watan Fabrairu 2025. Haka kuma idan aka duba wata-wata, hauhawar farashi a watan Maris 2025 ya kai kashi 3.90%, wanda ya fi na watan Fabrairu 2025 (2.04%) da kashi 1.85%.”

“Wannan yana nufin cewa a watan Maris 2025, ƙimar hauhawar matsakaicin farashi ya fi ƙimar da aka samu a watan Fabrairu 2025.”

Rahoton ya bayyana cewa ƙarin da wasu rukunnan kayayyaki suka yi wa hauhawar farashin sun haɗa da abinci da abin sha marasa giya, kashi 9.28%; gidajen cin abinci da wuraren masauki – 2.99%; sufuri – 2.47%; gidaje, ruwa, lantarki, iskar gas da makamashi – 1.95%; ayyukan ilimi – 1.44%; da lafiya – 1.40%.

Rahoton ya kuma bayyana cewa hauhawar farashin abinci a watan Maris 2025 ya kai kashi 21.79 cikin dari idan aka duba shekara zuwa shekara.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *