January 22, 2025

An Ba Wa Ganduje Wa’adin Kwanaki 7 Ya Sauka Daga Shugabancin Jam’iyyar APC.

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Wani jigo a jam’iyyar APC Alhaji Saleh Zazzaga, ya sabunta yunkurin tsige shugaban jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, ta hanyar neman ya sauka daga mulki cikin kwanakki bakwai.

Sabon yunƙurin na Zazzaga na zuwa ne a dai-dai lokacin da ya kasa samun nasara a yunƙurin sa na tsige Ganduje, ta hanyar yin ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, in da mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da ƙarar da ya shigar a ranar ashirin da uku ga watan Satumba bayan kotu ta ce kungiyar APC ta Zazzaga mai suna Arewa ta Tsakiya, ba ta da hurumin shigar da ƙarar.

Alkalin ya kuma bayyana cewa kungiyar ta gaza samar da hanyoyin warware rigingimun cikin gida na jam’iyyar kafin tunkarar kotun.

Daily Trust ta rawaito, a wata sabuwar wasiƙa Zazzaga a wata ya aikewa Ganduje, ya ce an yi hakan ne domin nuna ƙoƙarin da kungiyar ke yi na warware matsalar ta hanyar ruwan sanyi.

Rashin adalci ne a bada rabon tallafin shinkafar Kano a hannun APC – Kwankwaso.

APCin Kano Na Son EFCC Ta Yi Bincike Kan Bidiyon Ɗan Bello.

Da Gaske Ne Shugaban APC Ganduje Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa A Zaɓen 2027?

Da yake jawabi ga manema labarai a Jos babban birnin jihar Filato a jiya, Zazzaga ya bayyana cewa an aike da kwafin wasikar ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC), da kuma majalisar ba da shawara ta jam’iyyar APC.

Ya kuma jaddada cewa wa’adin kwanakki bakwai din za su fara ne daga ranar litinin, zai kuma kare a mako mai zuwa, ya kuma ce rashin yin hakan zai sa su ƙara daukar matakin shari’a.

A cewar Zazzaga sun yi amfani da hanyoyi daban-daban na cikin gida, tare da ci gaba da tattaunawa da ‘ya’yan jam’iyyar, amma Ganduje ya yi tsaye kai da fata wajen rike mukamin, wanda bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kujerar a yanzu ta yankin Arewa ta tsakiya ce.

Zazzaga ya kuma ƙara da cewa Ganduje ya na fuskantar shari’a kan zargin cin hanci da rashawa a jihar Kano, lamarin da a cewar sa ya na kara zubar da mutuncin jam’iyyar.

Ya yi kira ga Ganduje da ya gaggauta yin murabus domin dawo da dimokuradiyya da kuma mutunta yarjejeniyoyin karɓa-karɓa da jam’iyyar ta ƙulla.

Zazzaga dai ya bayar da shawarar cewa, Ganduje ya koma gefe ya bar kwamitin bincike ya binciki lamarin kamar yadda doka sashi na 21 sakin layi 3 na kundin tsarin mulkin APC ya tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *