An banka wa gidaje 24 da rumfunan ajiyar hatsi 16 wuta, yayin wani rikicin al’umma tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani a Gidan Na Ruwa da ke Karamar Hukumar Taura a Jihar Jigawa.
Jaridar PUNCH ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar a daren Litinin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar SP Shi’isu Adam, ya ce ‘yan sanda sun kai samame yankunan da abin ya shafa tare da cafke mutane biyar da ake zargi da hannu a rikicin.
Adam ya bayyana cewa matasa daga ƙauyen Zangon Maje ne suka kai harin, ya na mai cewa “Matasan da ake zargi suna ƙoƙarin kai ramuwar gayya ne, sun far wa mazauna yankin tare da banka wa gidaje da rumfunan ajiyar hatsi wuta.”
Ya ce, “Rikicin ya fara ne lokacin da wasu mutum biyu Musa Hussaini da Shanu Sule, dukkan su daga ƙauyen Zangon Maje aka lakaɗa masu duka tare da kwace musu babur, in da suka tara mutanen garin su domin yin ramuwar gayya.”
Adam ya bayyana cewa, “DPO na Taura da tawagar sa sun ɗauki matakin gaggawa bayan samun rahoton lamarin, in da suka isa wurin suka tarar da ɓarnar da aka yi. Yanzu an dawo da zaman lafiya, kuma ana ƙara sintiri a yankin domin hana sake aukuwar tashin hankali.”
Ya ce rundunar ‘yan sanda ta cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a rikicin, kuma suna taimakawa wajen bincike.
Ya gargadi al’umma da su daina ɗaukar doka a hannun su.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.
-
Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata.