Shugaban Jam’iar Abubakar Tafawa Balewa ATBU da ke Jihar Bauchi, Farfesa Muhammad AbdulAziz ya nemi a riƙa yiwa malaman jami’a gwajin shan kwaya ba iya ɗalibai ba kawai.
Ya yi wannan batu ne lokacin da yake bayanin bankwana ga majalisar jami’ar a jiya Juma’a.
Ya ce ” Ina ganin idan har za a riƙa yi wa ɗalibai irin wannan gwaji na shan kwaya, ina ganin mune ahaƙƙu da a yiwa, mu ma’aikata muma a mana ba kawai mu riƙa cewa a yi wa dalibai ba kawai.”
“Mu ma mu mika kanmu a yi mana wannan gwajin domin mu tsaftace jami’o’inmu. Halayen arziki na da muhimmanci a wurinmu baki ɗaya.
“Idan har za a umarci dalibanka da su je su yi wannan gwajin domin tabbatar da lafiyar kwakwalwarsu, ina ganin babu wani abun damuwa idan suka malaman an yi musu irin gwajin. Ina ganin wannan ce hanyar daya da za a tabbatar da komai a jami’o’i,” in ji Farfesan.
BBC Hausa
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.