Fiye da ‘yan Najeriya 956 ne aka dawo da su daga Libya a cikin farkon shekarar 2025 kawai, kamar yadda shugabar Hukumar ‘Yan Najeriya mazauna Kasashen Waje Abike Dabiri-Erewa ta bayyana.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan kafofin watsa labarai da Hulda da Jama’a da Tsare-Tsare na hukumar Abdur-Rahman Balogun ya fitar a ranar Litinin, yana mai jaddada cewa wannan kokarin yana daga cikin hadin guiwa da kungiyar kasa da kasa mai kula da masu yin ƙaura (IOM) a Najeriya, da Hukumar kula da ‘Yan Gudun Hijira da masu su yin ƙaura ta kasa.
A cikin bayanin, an bayyana cewa daga cikin wadanda aka dawo da su, 683 mata ne, 132 maza, 87 yara da 54 jarirai.
An dawo da wadanda suka yi tafiyar ne cikin sawu shidda daga Janairu zuwa Maris 2025.
Tafiyar guda shidda sun hada da 152 a ranar 28 ga watan Janairu, 145,180 da 159 a ranar 11, 19 da 25 na watan Fabrairu, yayin da 144 da 176 suka dawo a ranar 4 da 18 ga watan Maris.
A cikin shekaru kadan da suka gabata, fiye da yan Najeriya 15,000 da suka makale a kasashen waje aka dawo da su gida, ta hannun gwamnatin tarayya da hukumar kasa da kasa mai kula da masu yin ƙaura, kamar yadda sanarwar ta sanar.
Dabiri-Erewa ta sake jaddada shawarar da hukumar ke ba ‘yan Najeriya na guje wa hanyoyin ƙaurace-ƙaurace masu hatsari da cutarwa kamar Libya, kasa mai fama da yaki da matsaloli da dama.
Ta bukaci ‘yan Najeriya su rika bin hanyoyin hijira na doka, tana mai cewa wasu daga cikin ‘yan Najeriya da aka ceto daga Libya har yanzu sun sake komawa Libyar, ko kuma sun bi wasu hanyoyi masu hatsari domin shiga Turai.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja
-
Fasinjojin wata mota huɗu sun riga mu gidan gaskiya wasu kuma sun jikkata a jihar Borno.