Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wasu bayanai da ke fitowa daga birnin Kano na cewa Hukumar Karɓar korafe-korafe ta Jihar Kano, ta gano wani babban rumbun ajiya da ake sauyawa shinkafar tallafi ta Gwamnatin Tarayya buhu domin sayarwa.
Hikima Radio ta rawaito cewa an gano shinkafar ne a unguwar Hotoro da ke birnin Kano.
Gwamnan Abba ya zargi gwamnatin Ganduje da cin hanci da rashawa da gazawa wajen tsara birane.
Shinkafar wanda yawanta ya kai Tirela 23 na ɗauke da hoton Shugaba Bola Ahmad Tinubu wanda aka rubutu cewa shinkafar ba ta sayarwa ba ce.
A baya dai shugaba Tinubu ya aiko da shinkafa jihar Kano a wani mataki na rage wa al’umma raɗaɗin halin da suke ciki na matsin rayuwa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.