Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta fara farautar wasu matasa da ake zargi da daukar doka a hannun su, ta hanyar hallaka wani Dokagk Danladi da ake zargi da satar kare.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ahmed Wakili, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Wakil ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Bauchi Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan wannan mummunan aikin daukar doka a hannu da aka yi wa wani mutum mai suna Peter a ranar 9 ga watan Afrilu 2025, da misalin karfe 11:30 na dare.
“Lamarin ya shafi wani farmaki da wasu matasa suka kai wa wasu mutum biyu da ake zargi da satar kare.”
Wakili ya bayyana cewa wanda abin ya rutsa da shi, Dokagk Danladi mai shekara 38, wasu matasa ne suka kai masa hari a wani wuri da na mutane a bayan Lushi, bayan da aka zargeshi da sata.
Ya ce “Dokagk ya samu raunukka masu tsanani, ciki har da raunin adda a kansa, kuma an garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi domin kula da lafiyar sa.”
“Abokin sa Peter, wanda har yanzu ba a gano sunan mahaifin sa ba, an same shi a wurin da lamarin ya faru, kuma likitoci sun tabbatar mutuwar sa.”
Wakili ya ce ana ci gaba da bincike, kuma rundunar ‘yan sanda na kokarin gano duk wadanda suke da hannu a wannan aika-aika.
“Shugaban sashen ‘yan sanda na yankin (DPO) ne ke jagorantar tawagar jami’an bincike da ke ziyartar wurin da lamarin ya faru, domin tattara shaidu da fahimtar yadda lamarin ya kasance,” in ji shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya