Labarai
Trending

An Kammala Yarjejeniya Da Sabon Kocin Super Eagles Ta Najeriya.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta kammala yarjejeniya da Bruno Labbadia a matsayin kocin Super Eagles.

Babban sakataren NFF, Dr. Mohammed Sanusi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Safiyar a Yau Talata.

“Kwamitin zartarwa na NFF ya amince da shawarar naɗa Bruno Labbadia a matsayin babban kocin Super Eagles,” in ji Mohammed Sanusi.

A watan Yuni ne tsohon kocin ƙungiyar Finidi Geroge, ya aje aiki bayan naɗa shi a watan Afrilun da ya gabata.

Kafin Finidi George za zama koci shine mataimakin Jose Peseiro wanda shima tsohon kocin Najeriya ne da ya ajiye aiki, bayan ya yi aiki na tsawon watanni 20.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button