Daga Zainab Adam Alaramma
Wani rahoto da majalisar ɗinkin Duniya ta fitar na shakarar 2023 ya ce, har yanzu ana ci gaba da samun kisan mata a hannun abokan zamansu ko ‘yan uwansu, kuma matsalar na ƙara ƙaruwa a sassan duniya daban-daban.
BBC ta rawaito cewa, binciken ya nuna cewa a faɗin duniya baki ɗaya an kashe mata da ‘yan mata 85,000 da niyya a shekarar 2023.
Hukumar EFCC ta ba wa jami’anta umarnin bincikar gwamnonin da ke kan mulki.
Trump Na Gaba-Gaba A Sakamakon Zaɓen Amurka.
Amnesty Ta Nemi A Saki Ɗan PDPin Da Ke Tsare A Sokoto Kan Wallafa Bidiyon Gwamna Da Matarsa.
Matsalar ta fi kamari a yankin Afirka, in da ta kasance kan gaba wajen yawan cin zarafin mata, da takan kai har da kisan matan, a tsakanin abokan zama ko danginsu.
Ranar 25 ga watan Nuwamba dai ita ce ranar da Majilisar Ɗinkin Duniya ta waje domin yaƙi da cin zarafin mata.