April 1, 2025

An sace jami’in Hukumar Kiyaye Haddura ta Najeriya FRSC a jihar Benue

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen jihar Benue, ta tabbatar da sace daya daga cikin jami’an ta mai suna Insfekta Nathaniel Kumashe.

Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Ngozi Ahula, ita ce ta tabbatar da sace shi a ranar Alhamis a Makurdi, babban birnin jihar.

Ahula ta bayyana cewa, jami’in wanda ke aiki a Wannue cikin karamar hukumar Tarka, an sace shi ne da misalin karfe 10 na dare a ranar Laraba.

A cewar ta, an sace jami’in ne a garin su da ke Tse Aboh Uchi-Mbakor, bayan dawowar sa daga taron tunawa da dan uwan sa da ya rasu.

Ta ce, ‘’Yan bindigar sun harba bindiga domin razanar da iyalan sa da makwabtan sa kafin su tafi da shi.”

Ana zargin cewa wadanda suka yi garkuwa da shi sun kai shi wata mabuyar su da ke wata karamar hukuma da ba a bayyana sunanta ba a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *