January 22, 2025

An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

An yi arangama tsakanin makiyaya da wasu matasa a kauyen Lano da ke ƙaramar Hukumar Debo a jihar Gombe, in da aka samu asarar rai na mutum ɗaya yayin da biyu ke kwance a Asibiti.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar jihar Gombe ASP Buhari Abudullahi, in da ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ƴansandan jihar Gombe sun kama wasu matasa biyu bisa zargin fashi da makami.

Gwamnan Kaduna ya Ƙaddamar da Asibiti da Cibiyar Fasaha, shekara 1 bayan harin bam a ƙauyan Tudun Biri.

Sojan saman Nijeriya sun yi wa Ƴan Boko Haram fata-fata a Borno.

Da ya ke yi wa manema labarai ƙarin bayanin kan aukuwar lamarin ya bayyana cewa wasu fusatattun matasa ne da su ka fito daga ƙauyen Lano in da subka rufe titin da ya haɗa ƙauyen Lano da kuma Dabe tare da kai wa wasu makiyaya hari da suka taso daga ƙauyen Kuri, inbda su ka kashe musu shanu biyar wanda hakan shi ya haddasa tashin tarzomar.

Ya kuma ce matasan da ake zargin makiyaya sun kwacewa wasu daga cikin ƙananun manoma wayoyin hannu tare da amfanin gonar su.

Ya kuma bayyana cewa yanzu haka Ƴansanda sun kewaye yankin da abun ya faru domin dawo da zaman Lafiya a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *