April 1, 2025

An yi jana’izar Alhaji Nasiru Ahli a birnin Kano, in da al’umma ke alhinin rashinsa

Marigayi Alhaji Nasiru Ahli, ya rasu ne a daren ranar Juma’ar nan bayan ya yi fama da jin jinya.

Nasiru Ahli, ya na daga cikin fitattun attajirin Kano kuma shi ne shugaban kamfanin Mainsara & Sons.

Daily Nigerian ta rawaito marigayin ya rasu ya na da shekara 108 a duniya, kuma ya na gudanar da harkar kasuwanci daban-daban, ciki har da buga littattafai da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje da kwangila da gina gidaje da aikin sarrafa ƙarfe da sauransu.

Wasu al’ummar Kano da dama sun fara nuna alhini da rashin nasa.

Tini dai aka yi jana’izarsa a Masallacin Jumu’a na Nasiru Ahali da ke Kurna Asabe, da ƙarfe 1 na rana a yau Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *