April 5, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027

Jam’iyyar APC, ta musanta rade-radin da ke cewa akwai sabani tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, inda ta yi watsi da zancen cewa Tinubu na shirin sauya mataimakinsa gabanin zaben 2027.

Da ya ke zantawa da Daily Trust a jiya Alhamis , Daraktan Yada Labarai na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya ce wadannan rahotanni basu da tushe balle makama.

“Wannan jita-jita ce kawai maras tushe. Wadannan maganganu ne da bai kamata a dauke su da muhimmanci ba,” in ji shi.

“Ko da ace, a wani dalili, shugaba yana da niyyar sauya mataimakin sa, ba zai iya yin hakan shi kadai ba. Wajibi ne a tattauna da manyan jiga-jigan jam’iyya kafin daukar irin wannan mataki,” in ji Bala Ibrahim.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *