Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta sanar da mataimakin gwamnan jihar Jigawa kuma ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Umar Namadi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ranar Asabar.
BBC Hausa ta rawaito cewa Namadi ya lashe zabe a ƙananan hukumomi 26 daga cikin 27 na jihar.
Ya samu kuri’u 618,449 inda ya samu galaba a kan ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido da kuma NNPP Aminu Ibrahim wanda ya zo na uku.
Dan takarar PDP ya samu kuri’u 368,726 a yayin da ɗan takarar NNPP ya samu ƙuri’u 37,156.
Babban jami’in da ke kula da zaben, Farfesa Zaiyanu Umar ne ya sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi.