Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Shugaban jam’iyyar APC mai adawa a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya gargaɗi gwamna Abba Kabir Yusuf, da ka da ya kuskura ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi “kamar yadda wata kotu bayar da umarni.”
BBC ta rawaito, a wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar Juma’a a Abuja, Abdullahi Abbas ya ce ya kamata gwamna Kabir Yusuf ya san cewa idan har ya ci gaba da gudanar da zaɓen to “tamkar ya gayyato rashin zaman lafiya ne a jihar ta Kano.”
“Kawai gwamna ya bi umarnin kotu, a matsayinmu na masu son bin doka da oda da kuma son cigaban jiharmu ta Kano, dole ne gwamna ya guji duk abin da ka iya jefa jihar tamu cikin ruɗani.” In ji Abdullahi Abbas.
Rashin adalci ne a bada rabon tallafin shinkafar Kano a hannun APC – Kwankwaso.
Kotu: An Tsare Ɗan Jarida A Gidan Yari Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamnan Kano Abba.
Ƴan Kasuwar Man Fetur Sun Fara Siyen Man Daga Matatar Dangote.
Wannan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i kaɗan a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Kano mai cike da turka-turka.